Accessibility links

Kwararru sun bayyana damuwa game da sabon maganin yaki da cutar kanjamau


kwalbar maganin yaki da cutar kanjamau
Kwararru a fannin kiwon lafiya musamman a kasashen nahiyar Afirka sun bayyana damuwa game da sabon maganin yaki da cutar kanjamau da cibiyar kula da ingancin magunguna da abinci ta Amurka ta bada izinin amfani da shi.

Shugabar farko ta cibiyar yaki da cutar kanjamau a Najeriya farfesa Ibironke Akinsete ta bayyana cewa, amfani da maganin truvada wajen kare wadanda basu dauke da cutar daga kamuwa da ita, ba wani abu zai haifar ba illa karfafa mutane su shiga shashanci.

Farfesa Akinsete ta bayyana damuwa cewa, gabatar da wannan maganin zai kawo koma baya a al’umma musamman tsakanin matasa wadanda basu kula da irin rayuwarsu ba. Bisa ga cewarta, idan mutane suka san amfani da maganin zai karesu daga kamuwa da kwayar cutar kanjamau, zasu yi ta aikata jima’I barkatai.

Jami’ar kiwon lafiyar ta shawarci kasashe musamman Najeriya da kuma kwararru a fannin kiwon lafiya, su nemi matakan shawo kan yada cutar da zasu zama da karbuwa da kuma taimako ga rayuwar al’umma.

Truvada, wani sabon magani ne da kwararrun kiwon lafiya a kasar Brazil suka sarrafa da Amurka ta amince a yi amfani da shi, tsakanin wadanda basu dauke da cutar da ke cikin hatsarin kamuwa da cutar, sabili da mu’amala da wadanda ke dauke da cutar su yi amfani da shi domin kare kansu.
XS
SM
MD
LG