Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lantarki na ciwa masu sana’o’i tuwo a kwarya a Neja


Tambarin Kamfanin Samar Da Wutar Lantarki a Najeriya
Tambarin Kamfanin Samar Da Wutar Lantarki a Najeriya

Matsalar wutar lantarki ta dade tana ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, wanda hakan sai da ta kai ga sayar da hukumar wutar lantarkin kasar ga ‘yan kasuwa.

To wannan matsala ta addabi masu kananan sana’o’in hannu da suke amfani da wutar lantarki. Wanda suka hada da masu aski, walda da kuma shaguna.

Babbar matsalar da suka fi kokawa a kai it ace, yadda kullum ake faman cewa ta lalace sai an yi gyara anan da can da kullum aikin Kenan ba biyan bukata.

Bayan ta bakin masu sana’oin, shima shugaban kamfanin kula da hasken wuta na Kainji da Jaba Kanar Sani Bello mai ritaya yace akwai matsaloli. A saurari rahoton da ke makale don jin cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG