Accessibility links

Manyan 'Yan Takarar Shugabanci A Kenya Sun Kammala Yakin Neman Zabe.

  • Aliyu Imam

'Yan takarar shugabancin Kenya daga hagu: Uhuru Kenyatta, Peter Kenneth, Musalia Mudavadi, Martha Karua, and Raila Odinga, da wasu 'yan takara da ba a gansu ba a hoton nan, a wata mukabala da suka yi.
A Kenya manyan ‘yan takara a zaben shugaban kasa da za a yi gobe litinin sun gudanar da gangamin yakin neman zabe na karshe, inda PM Ra’ila Odinga da abokin takararsa mukaddashin PM Uhuru Kenyatta suke ta sukar juna.

Mr. Odinga ya karyata wani rahoto a wata jaridar Ingila Financial Times cewa yayi ikirarin tada tarzoma shigen wacce ta faru a 2007, idan abokin takararsa yayi magudi.

Mr. Odinga yace rahoton bashi da tushe. Yace baita ba cewa za a tada tarzoma a Kenya ba.

Mr. Uhuru Kenyatta, da mataimakinsa William Rutto, wadanda dukkansu biyu kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffuka ta gabatar da tuhuma akansu kan zargin tada tarzomar da ta biyo bayan zaben 2007 a Kenya.

Mr. Kenyatta ya roki masu zabe kada su maida hankali kan abinda yace kokarin abokin takararsa na neman bata masa suna.
XS
SM
MD
LG