Shugaba Emmanuel Macron ya isa kasar Mali inda ake sa ran zai halarci taron koli a kan kafa wata rundunar yanki ta yakar ‘yan ta’adda a Sahel.
Kasashen Mali, Burkina Faso, Chadi, Mauritaniya da kuma Nijar, wadanda ake kira G-5 Sahel, sun ce zasu hada karfi su kafa rundunar hadin guiwa da zata yaki tabarbarewar tsaro da ‘yan ta’adda dake kara kunno kai a yankin.
Rundunar ta G-5 Sahel zata kara karfafa ayyukan sojoji dubu 4 na Faransa da kuma waszu dubu 11 na Majalisar Dinkin Duniya dake aikin kiyaye zaman lafiya yanzu haka a yankin.
Ana sa ran Macron zai bayyana cikakken goyon baya da tallafin Faransa ga kafa wannan runduna ta yanki. A yanzu haka dai ba a san irin tallafin da Faransa zata ba wannan runduna ba.
A watan Mayu, Macron ya ziyarci birnin Gao dake arewacin Mali, ziyararsa ta farko a wajen nahiyar Turai tun zamowarsa shugaban Faransa. A wurin ya bayyana cewa sojojin Faransa zasu ci gaba da zama har sai an ga bayan ayyukan ta’addanci a yankin.
Facebook Forum