Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahathir Mohammed Ya Hana Najib Razak Fita Daga Kasar Malesiya (Malaysia)


Mahathir Mohammed

Kamar yadda aka zata zai faru, an fara takun saka tsakanin sabon Firaministan Malesiya da tsohon Firaminista kan zargin almundahana da kuma makomar kasar

Sabon Faraministan Malaysia ya fadi yau Asabar cewa shi ya hana mutumin da ya gada fita daga cikin kasar.

Mahathir Muhammad ya ce shi ya hana tsohon Faraminista Najib Razak da matarsa fita daga kasar. Kafar labarai ta Associated Press ta ce wata takardar rajistar matafiya ta nuna cewa da Najib da matarsa sun yi yinkurin fita daga kasar zuwa Jakarta a wani jirgin sama samfurin jet wanda ba na fasinja ba.

Mahathir, dan shekaru 92 da haihuwa, ya ce gwamnati ta samu isasshiyar shaidar da ke nuna cewa Najib na da hannu dumu-dumu a wata babbar tabargazar cin kudi.

Najib ya sanar a kafar FaceBook cewa za shi hutu, amma bai dawo bayan mako guda, abin da ya janyo rade-radin cewa so ya ke ya gudu da wayo don ya kauce ma fuskantar shari’ar.

Najib dai ya ce shi fa bai aikata wani laifi ba.

Haka zalika a yau din Asabar diyar Anwar Ibrahim ta gaya ma kafafen yada labarai cewa za a saki jagoran ‘yan adawar daga gidan yari ranar Talata kuma ya a masa cikakkiyar ahuwa ta mutunci.

An jefa Anwar fursuna ne kan tuhumar almundahana da kuma luwadi wanda da dama ke ganin bita da kullin siyasa ne kawai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG