Accessibility links

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana kisan Yahudawa da dama da Hitila yayi, (wato Holocaust a Turance), da cewa laifi ne mafi muni da aka taba yi ga bil'adama a wannan marra.

An wallafa wannan bayanin na Mr Abbas a yau dinnan Lahadi a wata jaridar hukumar Falasdinawa mai suna WAFA a takaice, 'yan sa'o'i kafin Isira'ila ta fara hidimar zagayowar ranar kisan na kare dangi, kuma 'yan kwanaki bayan da aka dage tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isira'ila da Larabawa.

Ba kasafai shugabannin Larabawa kan jaddada wahalar da Yahudawa su ka sha a yayin kisan kare dangin na Nazi irin yadda ya yi a bayanin nasa ba. Yahudawa dai miliyan shida aka hallaka a wannan kisan kare dangin na Holocaust.
XS
SM
MD
LG