Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Diinkin Duniya ta Bukaci Birnin Detroit Ya Mayarda Ruwabn da Ya Yanke


Birnin Detroit

A wani abun da ba'a taba gani ba Majalisar Dinkin Duniya ta ziyarci birnin Detroit dake fama da dimbin bashi inda da ta umurci mahukuntan birnin su mayar da ruwan da suka yanke daga gidajen mutane marasa galifu

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga jami’an birnin Detroit dake jihar Michigan a arewacin Amurka, su bada ruwa ga mutane da suka kasa biyan kudin ruwa da hukumomi suke binsu a yankin.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya Catarina de Albuquerque, da Leilani Farha, jiya Litinin suka kammala ziyarar aiki ta kwanaki uku da suka kai birnin, inda suka sadu da wadanda matakin ya shafa, da masu rajin kare hakkin Bil’adama, da kuma jami’an karamar hukumar Detroit.

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun ce matakin hana ruwan, yafi shafar marasa galihu wadanda suka kasance bakar fata, kuma hakan ya tilastawa mutanen zabi, tsakanin biyan kudin haya ko kuma na ruwa.

Birnin Detroit ya katse ruwa ga fiye da mutane dubu 27 bana.

Karkashin sharuddan hukumar, duk wanda bai biya kudin ruwan da yayi amfani dashi ba har ya kai wata biyu, za’a iya dakatar da bashi ruwa, a yunkurin da mahukuntan yankin suke yi na rage tulin bashi da ake bin birnin.

XS
SM
MD
LG