Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Matasan Musulman Najeriya Ta Lashi Takobin Dakile Rigingimu


Muslim youths praying

Yayinda majalisar matasa musulmi ta Najeriya ta kammala taron koli a Abuja babban birnin Najeriya t akudiri aniyar kawar da rigingimun da suka addabi kasar.

Taron ya tattaro matasan musulmai daga sassa daban daban na jihohi 19 dake arewa.

Taron ya duba kalubalen da kasar ke fuskanta da kuma bullo da sabbin dabarun magance matsalolin.

Injiniya Alhed Yakubu Jimba mataimakin shugaban kungiyar ta kasa kuma mai kula da jihohin arewa yace duk rayuwar da ba'a sama mata matsaya ba to an maida ita kayan aikin Shaidan. Akwai bukatar iyaye su yiwa 'ya'yansu tarbiya ta kwarai.Dole ne kuma malaman addini su tashi su yi fada, wato su dinga tsawatawa. Sarakuna ma su tashi su yi fada. Gwamnati ma ta samarda yanayi da zai bada damar yin aiki. A koyawa matasa sana'o'i.

Mai masaukin baki Sani Suleiman Maigoro kuma sakataren kungiyar na jihohin arewa yace taron ba na shan shayi ba ne.

Yace hadin kai shi ne na farko. Yace suna da matsala dukansu kuma dukansu suna da rawar da zasu taka. Matukan ba'a sa matasa bisa sahihin addini ba to akwai matsala. Saboda haka malamai su mayar da hankali wajen samarda ilimi ingantace da zai dora matasa akan fahimtar addini.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG