Accessibility links

Majalisar dokokin kasar Somaliya tana aikin shimfida sabuwar gwamnati


Wakilan majalisar tsarin mulkin kasar Somaliya
Yau ne majalisar dokokin kasar Somalia take komawa bakin aikin shimfidawa kasar sabuwar gwamnati da ake fatar zata kasance ingantacciya ce kuma mai karko.

Tuni wani kwamiti ya zabar wa majalisar wakilai 225, koda yake kujeru 275, amma jami’ai sunce wadanan ma na yanzu sun isa su soma wannan gagrumin aikin.

A cikin tadin da yayin da sashen Somaloyanci na VOA, ministan harakokin tsarin mulki da Sulhuntawa na kasar, Abirahaman Hoshi Jibril yace wadanan sababbin wakilan zasu zabar kansu sabon kakaki da mataimaknsa kafin ran 27 ga watan nan, sannan a farkon wata mai fita na satumba kuma a zabi sabon shugaban kasa.

A da a yau Litinin ne Majalisar Dinkin Duniya ta yankawa Somalia wa’adin zaben kakakin majalisar har ma da sabon shugaban kasa a karkashin yarjejeniyar da aka kulla don a kai kasrhen mulkin shekaru takwas da gwamnatin rikon kwarya ta yi tana jan ragamar harakokin kasar, amma ga alama bukatar cimma wannan wa’adin ba zata samu a yau din ba.

Duk da haka ita Majalisar Dinkin Duniya da kasashen da take aiki da su duk sun fito da sanarwar dake wa kasar kyakyawar fatar Alheri da bayyana karfin gwiwar cewa wannan shirin zai kai Somalia ga samun dawammamen zaman lafiya.
XS
SM
MD
LG