Accessibility links

An Yi Taron Fadakarwa wa Mahajattan 2014


Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsari a Saudiya.

Kowace shekara yawancin mahajatta daga karkara sukan samu damuwa yayin aikin hajji domin rashin fahimtar wasu abubuwa, dalili kenan da hukumar aikin alhazai ta shirya taron fadakar da kai.

Taron da aka yi, an shiryashi ne domin a fadakar da ma'aikatan aikin hajji na jihohi domin su kokarta wajen fahimtar da mahajatta da niyyar su samu aikin hajji.

Alhaji Uba babban jami'in hukumar alhazai yace "sau da yawa mahajatta suna zuwa kasa mai tsarki ba tare da sanin dalilin da ya kaisu ba, ko kuma basu san yadda zasu yi aikin hajjin ba. Misali idan an dauki mutumin karkara da ko babban birnin karamar hukumarsa bai taba zuwa ba aka sashi jirgi ya sauka a Saudiya inda akwai wutar lantarki koina sai ya rikice. Wasu kuma har toci suke tafiya da ita domin tsoron kada a dauke wuta kamar yadda ya saba gani a Najeriya. To ire-iren wadannan mutanen dole a wayar da kawunansu."

Alhaji Uba ya kara da cewa "haka kuma yakamata a horas da su domin su sani duk abun da suka yi zasu dawo kasarsu. Idan sun yi abun kunya kasarsu suka shafawa kashin kaji. Sabili da haka haki ne akan hukumar alhazai ta wayar da kawunan mahajatta domin su samu ladan aikin da zasu yi."

"Za'a kuma koyawa mahajattan da basu taba fita daga kauyensu ba kuma basu taba shiga jirgin sama ba. Dole su san yaya ma zasu shiga jirgin. Yaya zasu yi anfani da bayan gida irin na zamani? Ban da haka akwai dokokin kasa kashi kashi kuma yaya zasu kiyayesu? Ya zama wajibi a wayar da kawunan mahajatta domin su samu su yi cikakken aikin hajji", a cewar Mr. Uba.

Da wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya ya jawo hankalin Alhaji Uba akan sakacin wasu jami'an hukumar alhazai, musamman na jihohi inda sai su bar wasu alhazai suna yawo har su bata, su galabaita kafin a ganosu. Sai yace suna da matsalar kuma babbar matsala ce amma suna nanatawa jami'an jihohi su kara kuzari domin su shawo kan lamarin, domin a wasu lokutan sai a ga alhazai amma babu ko jami'in jiha daya da zai kula da su, an barsu kara zube. Cikin 'yan shekarun nan akwai dan canji amma har yanzu akwai sauran rina a kaba shi yasa suna rokon jami'an jihohi su yiwa Allah da Annabinsa su taimaki alhazansu su samu aikin hajji, su dinga taimaka masu inda basu gane ba su sasu a hanya.

Ga rahoto.
XS
SM
MD
LG