Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoma Suna Kokawa Akan Annobar Tsutsa A Gonakinsu


Rahotanni daga Najeriya na cewa wata tsutsa ta mamaye amfani gona irinsu masara da gero da dawa da kuma shinkafa a wasu sassa na kasar.

Yanzu haka dai hankalin manoma na kara tashi biyo bayan bullar wata tsutsa mai cin hatsi dake mamaye gonakin manoma a wasu jihohin kasar.

Alhaji Hamman Adama Ahidjo, daya daga cikin manyan manoman Adamawa ya ce tsutsar ta yi mummunar barna a gonaki musammam waɗanda shukarsu ba ta yi ƙwari ba.

Shima shugaban kungiyar Manoman Nyokore Abdur Razaq Sarkin ruwa ya ce tsutsa da ke mamaye gonaki ta fantsama kan shukar manoma musammam amfanin gona irinsu masara da gero da dawa da kuma shinkafa, kuma kawo yanzu ba wani mataki da gwamnatin jihar ta dauka.

Kamar jihar Adamawa suma manoman jihar Taraba,tuni suka fara kokawa. Sa’adu Wangara- wani dattijo a jihar Taraba da tsutsan suka barnatawa gona, yace abinda da tsutsar ke yiea gonaki na da bantsoro.


To wai ko wani irin illa wannan tsutsar ke da shi a yanzu? Mallam Abdullahi Musa malami ne a sashin koyon dabarun aikin gona na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa, wato SPY-Yola, cewa yayi da zarar manomi ya fara ganin kwari a gona to yakamata yafara feshi da safe dakuma yamma shine dai dai a sa magani a gona.
Gwamnatin Najeriya dai da ta tabbatar da bullar wannan tsutsa da tace za’a kashe kusan Naira biliyan uku (N2.98 billion) domin gudanar da feshi a gonaki murabba’in kadada wato hecta 700,000 a fadin kassar.

Kawo yanzu dai manoman jihohin sun kasa suna jiran daukin da gwamnatocinsu zasu yi, yayin da al’umma ke komawa gona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:24 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG