Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu kada kuri'a suna zaben gwamnoni a jihohi uku na kasar Mexico.


Zanen jam'iyar PRI dake takara a zaben gwamnoni uku na kasar Mexico.

Masu kada kuri’a a kasar Mexico sun yi tururuwa zuwa runfunan zabe yau Lahadi domin zaben gwamnonin jihohin Mexico da Coahuila da kuma Nayarit.

Masu kada kuri’a a kasar Mexico sun yi tururuwa zuwa runfunan zabe yau Lahadi domin zaben gwamnonin jihohin Mexico da Coahuila da kuma Nayarit. Binciken ra’ayoyin jama’a dangane da zaben na nuni da cewa, ‘yan takarar jam’iyar Intitutional Revolutionary-PRI sune kan gaba da na jam’iyar shugaba Felipe Calderons Conservatice National Actio –PAN. Jam’iyar PAN tayi kokarin hada kai da jam’iyar Democratic Revolution –PRD da zumar kada jam’iyar PRI a Nayarit da Coahulla sai dai har yanzu ‘yan takararta ne suka fi kwarjini a zaben da za a gudanar yau Lahadi. Gwamnan jam’iyar PRI na yanzu a jihar Mexico, Enrique Pena Neito ne ake gani zai yi tasiri a takarar shugaban kasa badi. Jihar Mexico ce jihar da tafi yawan al’umma a kasar. Yana yiwuwa Pena Neito ya tsaya takara da shugaba Calderon wanda masu sharhi kan lamura suka yi harshashen cewa, zai iya faduwa zabe a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu sabili da yawan tashin hankali dake da nasaba da masu safarar miyagun kwayoyi sun dushe farin jininshi da kuma ikon fada a ji da yake da shi a jam’iyarshi. Dubun dubatan mutane sun mutu sakamakon tashe tashen hankalin da ke da alaka da safarar miyagun kwayoyi tunda Mr. Calderon ya hau karagar mulki cikin shekara ta dubu biyu da shida ya fara yaki da fataken miyagun kwayoyi.

XS
SM
MD
LG