Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata na Korafi a Siyasar Adamawa


An bukaci ‘yan takarar Gwamna a jihar Adamawa dasu zabi mata, a matsayin mataimakansu idan har suna bukatar kuri’un mata a zabe mai zuwa.

Hajiya Hadiza Ningi, ce ta furta haka a wani gangamin da kungiyoyin mata suka gudanar domin ganawa da manema labaru a Yola babban birnin jihar Adamawa, ciki har da wakilin muryar Amurka, Ibrahinm Abdulazeez.

Ta kara da cewa duniya yanzu a ci gaba tafiyar da ake yi sai da mata, ta na mai cewa suna da mata masu ilimi da kwazo, bata ga dalilin da zai sa ba a dauki mace a matsayin mataimakin gwamna ba.

Jam’iyu goma sha biyu ne suka tsayarda ‘yan takarar Gwamna, a jihar Adamawa, cikin su harda mace daya mai son fafatawa da maza a faggen zabe.

Siyasar Adamawa - 3'29"
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG