Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar yunwa na kara tsananta a Sudan ta Kudu


Likita na duba wani yaro daga cikin 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
Likita na duba wani yaro daga cikin 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya tace tashin hankali kuma rashin kyaun damina a Sudan ta Kudu ya jefa miliyoyin mutane cikin hadarin yunwa.

Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin da ake fama da shi da kuma rashin kyaun damina a Sudan ta Kudu ya jefa miliyoyin mutane cikin hadarin yiuwar fama da yunwa.

Wata sanarwar hadin guiwa tsakanin shirin samar da abinci na duniya (WFP) da kuma cibiyar harkokin noma (FAO) yana nuni da cewa, adadin wadanda basu da isasshen abinci a Sudan ta Kudu ya haura zuwa miliyan hudu da dubu dari bakwai, karin kashi arba’in bisa dari.

Binciken ya kuma bayyana cewa, daga cikin adadin, kimanin mutane miliyan daya suna bala’in bukatar tallafin abinci. Sai dai ya yi gargadi da cewa, adadin na iya karuwa sabili da tsadar abinci da kuma kaurar mutane sakamakon tashin hankalin da ake yi a yankunan biyu.

Binciken ya kuma ce, kamfan ruwa da aka samu ya haddasa rashin kyaun damina, abinda kuma ya sa farashin kayan masarufin suka yi tashin gwauron zabi.

Bisa ga rahoton ci gaban kasuwanni kamar yadda aka saba zai taimaka wajen samar da abinci, sai dai rufe kan iyakokin da makwabciya Sudan da aka yi ya shafi kasuwanni.

XS
SM
MD
LG