Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Al-Shabab Su Na Tserewa Daga Kismayo


Mayakan kungiyar al-Shabab ta Somaliya

Wani kwamandan sojojin Somaliya, yace dakarunsu sun ragargaza layuka da shingayen tsaron da kungiyar al-Shabab ta girka a birnin Kismayo

Wani kwamandan sojojin gwamnatin Somaliya, yace dakarun gwamnati da na Kungiyar Tarayyar Afirka sun ragargaza layuka da shingayen tsaron da kungiyar al-Shabab ta girka a birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa, kuma mai muhimmanci ga kungiyar.

Kanar Yasin Noor, ya fadawa Muryar Amurka daga bakin daga yau talata cewa sojoji masu goyon bayan gwamnati su na kauyen Jana Abdalle, kimanin kilomita 60 daga birnin Kismayo, kuma su na shirin shiga birnin na da kwana daya ko biyu.

Kanar Noor yace a yanzu kusan babu mayakan al-Shabab dake kare birnin.

Kismayo shi ne birni na karshe da ya rage a hannun 'yan al-Shabab a Somaliya.

Shaidu sun ce mayakan al-Shabab sun fara janyewa daga birnin Kismayo ranar lahadi, su na kawar da manyan makamansu zuwa wasu garuruwa dake kusa da nan.

Kakkin wata kungiyar sojojin sa kai mai goyon bayan gwamnati, yace a yau talata, ba su ga mayakan al-Shabab su na gadin shingayen tsaron da suka kakkafa a kewayen birnin ba.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da dubu biyu sun gudu daga birnin Kismayo daga ranar lahadi zuwa yanzu.

Kismayo yana da matukar muhimmanci ga al-Shabab saboda yana ba su damar shigowa ko fita da wani abu ta tashar jirgin ruwa, sannan yana kusa da wani makeken gandun daji inda kungiyar take da sansanonin horas da mayaka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG