Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Dole A Gudanar Da Binciken Kwakwaf Akan Cin Zarafin Kabilar Rohingya A Myanmar


Tawagar MDD a Myanmar

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya dake ziyara a kasar Myanmar ta ce wajibi ne a aiwatar da binciken kwakwaf akan ayyukan ashshan da aka aikata a kasar inda aka ci zarafin kabilar Rohingya aka tilasta masu ficewa daga jihar Rakinde bayan an kashe dubbansu

Wata babbar tawagar Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta fada a jiya Talata cewa wajibi ne, a gudanar da binciken kwa-kwaf akan ayyukan ashshan da ake aikatawa kan ‘yan kabilar Rohingya na kasar Myammar.

Wakilan kwamitin sulhu na MDD wanda shine tawaga mafi girma da tasiri ya kai ziyara a jihar Rakine dake kasar ta Burma tun a cikin watan Agusta, lokacin da rikicin da akeyi a kasar ya tilasta musulmai har sama da dubu dari 7 barin muhallan su zuwa makwabciyar kasar Bangladesh.

Sai dai Amurka da MDD sun kira wannan danyen aikin da akeyi kan jinsin ‘yan Rohingya wani yunkurin kakkabe su daga doron kasa.

Jakadun da suka kai wannan ziyarar sun gana manyan jami’an gwamnatin kasar ta Burma ciki ko harda shugaba Aung San Suu Kyi, da babban hafsan sojankasar Janar Min Aung Hlaing.

Sun tattaune kuma domin samun tabbacin cewa idan ‘yan kaar dake gudunhijira sun dawo kasar sub a zasu sakehuskantar wata barazana ba.

Jakadun dai sun bukaci jami’an gwamnatin ta Burma dasu sa hannu akan wata yarjejeniyar fahintar juna tsakanin su da MDD domin tabbatar da ayyukan sake dawo da ‘yan gudun hijiran ba tare da tsangwama ba, kuma domin kashin kansu kana cikin mutunci.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG