Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Na Kokarin Hana Kasar Sudan ta Kudu Fadawa Mawuyacin Hali -Guterres


Antonio Guterres babban sakataren MDD
Antonio Guterres babban sakataren MDD

Sabon sakataren Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, Antonio Guterres, yace Majilisar tana iya bakin kokarin ta domin ganin kasar Sudan ta Kudu bata fada cikin halin wayyo ni Allah ba.

Guterres yana magana ne da manema labarai a hedkwatar ta MDD dake birnin New York jim kaddan bayan dawowarsa daga taron kungiyar hada kan kasashen Africa (AU) wanda aka kammala a babban ofishin ta dake Adis Ababa na kasar Ethiopia.

Guterres yace ofishin sa zaiyi iya bakin kokarin sa domin ganin an samu masalaha ga rikicin na kasar Sudan ta Kudu cikin ruwan sanyi.

Yace daga dan abinda ya sani game da kasar Sudan ta Kudu mutanen suna bukatar zaman lafiya mai dorewa.

Sakataren naMDD yace sailin da yake rike da mukamin kwamishinan kula da ‘yan gudun hijira, abu na farko da ya fara yi shine ya tafi kasar Uganda inda ya halarcibikin ranar yan gudun hijira ta duniya da ‘yan kasar ta Sudan ta Kudu, inda suka taimakwa ‘yan kasar su dubu 500, domin su koma gida lokacin da aka kirkiro kasar, kuma sun tafi ne cike da doki da farin ciki.

Sai dai kuma yace samar da zaman lafiya mai dorewa zai dogara ne ga aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma na shekarar 2015 wanda zai kawo kowa da kowa cikin batun kamar yadda shugaba Salva Kirr ya bayyana.

Yace haka kuma kungiyoyi da hukumomi irin su MDD, kungiyar tarayyar Africa, AU da kungiyar nan da ake kira IGAD kowa nada rawar da zai taka kan wannan lamari.

XS
SM
MD
LG