Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Tsaron Somaliya da Babban Kwamandan Dakarun Kasar Sun Yi Murabus


Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed Famajo

Ministan tsaron Somaliya tare da babban kwamandan rundunar sojin kasar da ke jagorantar fada da mayaka masu tsatsauran kishin addini, sun yi murabusa daga mukamansu.

Yayin wata hira da Muryar Amurka, ministan yada labaran kasar, Abdurahman Omar Osman, ya ce ministan tsaron kasar Abdirashid Abdullahi Mohammed da kuma shugaban dakarun kasar Janar Mohammed Ahmed Jimale, sun mika takardun ajiye ayyukansu yayin taron majalisar gwamnatin kasar da ake yi a kowane mako.

A cewar ministan yada labaran, dukkansu sun ce dalilin ajiye ayyukansu abu ne da ya shafe su na kashin kansu.

Bayan taron majalisar, babu daya daga cikinsu da ya gana da manema labarai.

To amma wasu majiyoyin gwamnati da dama, wadanda suka nemi kada a ambaci sunayensu, domin ba a ba da umurnin wani ya yi magana akan al’amarin ba, sun ce ana samun rashin jituwa ne tsakanin jagororin biyu.

Wasu sun ce an jima ana korafi, kan yadda ake samun rashin hadin kai a tsakanin jami’an biyu.

Rahotanni sun ce tuni, shugaban kasar Mohammed Abdullahi Farmajo, ya maye gurbin shugaban dakarun kasar da Janar Abdi Jama Hussein.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG