Accessibility links

A yayin da ake ci gaba da nuna fusata a manyan biranen al-Qahira da al-Askandariyya kan hukumcin da kotun kolin kasar ta yanke ran alhamis.

A yau asabar da gobe lahadi Misrawa suke zaben shugaban kasa a tsakanin tsohon firayim minista Ahmed Shafiq da dan takarar kungiyar Ikhwanul Muslimun, Mohammed Morsi.

Za a yi wannan zabe cikin rudun siyasa, a bayan wani hukumcin da kotun koli ta yanke ta soke wata dokar da majalisar dokokin kasar sabuwa wadda ‘yan kishin Islama ke shugabanci ta zartas da ta haramtawa manyan jami’an hambararriyar gwamnatin Hosni Mubarak, kamar Mr. Shafiq, rike wani mukami a kasar. Har ila yau, alkalan kotun kolin sun bukaci da a rushe majalisar dokokin, su na masu kafa hujja da wasu matsalolin shari’a da aka fuskanta a zaben majalisar dokoki na baya.

Wasu jigogin islama sun zargi majalisar mulkin soja da laifin yin amfani da kotun domin yin juyin mulki a fakaice. Amma majalisar ta ce za a gudanar da zaben shugaban kasa kamar yadda aka shirya.

A lokacin da yake magana da magoya bayansa ranar alhamis a al-Qahira, Mr. Shafiq ya bayyana hukumcin kotun a zaman na tarihi ya kuma bukaci dukkan ‘yan Masar da su kada kuri’unsu. Amma kungiyar Ikhwanul Muslimun ta ce hukumcin kotun ya nuna cewa Masar ta doshi wani mawuyacin lokaci mai hatsari fiye da kwanakin karshe na mulkin Mubarak.

‘Yan zanga-zangar da suka fusata da wannan hukumci sun bazu a kan titunan biranen al-Qahira da al-Askandariya a jiya jumma’a domin nunawa duniya matsayinsu.

XS
SM
MD
LG