Accessibility links

Hotunan Tarihi Na Martin Luther King Jr. Jagoran Neman Hakkin Bakar Fata Na Amurka

Wasu Hotunan Tarihi Na Martin Luther King Jr. Jagoran Neman Hakkin Bakar Fata Na Amurka.
Bude karin bayani

1965 - Martin Luther King, Jr. a lokacin da yake jawabi a garin Selma, Jihar Alabama ran 12 Fabrairu, 1965. King yayi gwagwarmaya da jami'in tsaro na Selma, watau Sherrif, Jim Clark, game da batun 'yancin jefa kuri'a da rajistar bakake a zaman masu jefa kuri'a a Selma.
1

1956 - A ranar 23 Fabrairu 1956, Martin Luther King, Jr., tare da Rev. Ralph D. Abernathy sun mika kawunansu ga jami'in 'yan sanda Lt. D.H. Lackey a Montgomery, Jihar Alabama, bayan da aka tuhume su da haddasa yamutsi dangane da gangamin kauracewa shiga bas-bas na birnin.
2

1956 - Mai dakin Martin Luther King, Jr., Coretta, tana masa marhabin bayan da ya fito kotu a birnin Montgomery ta Jihar Alabama ranar 22 Maris, 1956. Kotu ta same shi da laifin shirya gangamin kauracewa shiga bas-bas na birnin a saboda yadda ake ce bakaken fata sai a baya zasu zauna, turawa kuma a gaba.
3

1962 - Wasu malaman addini daga jihohin arewa su na tafa ma shugaban majalisar shugabannin coci-coci na jihohin kudu,m Martin Luther King Jr. a lokacin da yake jawabi cikin wata majami'a a Albany, Jihar Georgia a ranar 28 Agusta, 1962.
4

Domin Kari

XS
SM
MD
LG