Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mota Ta Murkushe Matasa Goma Sha Hudu A Filato


Wani da mota ta buge

Mota ta murkushe matasa goma sha hudu har lahira a jihar Filato

Rundunar 'yan sanda a hijar Filato ta tabbatar da mutuwar matasa a wani hadarin mota da ya auku a wani kauye tsakanin Barkin Ladi da Bokkos.

Hadarin motar ya faru ne yayin da matasan 'yan birigedi dake attisahi da wata mota shake da masara a kan hanayarta ta zuwa kasuwar Bukuru ta auka masu. Nan take ta kashe goma sha hudu a cikinsu wasu kuma da dama suka samu raunuka. Bayan aukuwar lamarin direban motar ya yi ta kare. Yanzu 'yan sanda suna binciken hatsarin kuma sun shiga neman direban.

Yayin da ake kokarin taimakan wadanda suka ji ciwo da karaya motoci dake wucewa hanyar kin tsayawa suka yi. Sun ki su taimaka a kai mutane asibiti. Shugaban wata mijam'a da suka rasa matasa goma ya ce sun yi tawakali ga Allah. Ya ce sun rungumi kaddara.

Kawo yanzu dai ba'a samu direban motar ba kuma ana cigaba da kwantar da hankalin matsan da suke so su tayar da rigima su soma tare motoci. An shirya a yi jana'izar matasan da suka rasa rayukansu ranar Talata mai zuwa.

Zainab Babaji nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG