Accessibility links

Wata kungiyar hada kan Musulmai da Kiristoci a jihar Kaduna ta shiga bikin Mauludi domin taya Musulmai murnar wannan ranar.

Kungiyar wanzar da zaman lafiya da sasantawa tsakanin Musulmai da Kiristoci ta ce fahimtar dake tsakanin Musulmai da Kiristoci na kara ingantuwa.

Shugaban kungiyar Pastor Yohana Buru da yake jawabi a wani taron da ya shirya na taya Musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Mohammed (S.W.A.) a jihar Kaduna ya ce kyakyawar fahimta dake tsakanin mabiya addinan biyu ta sa duk lokacin da abun farin ciki ya samu daya to dayan kan zo domin ya tayashi murna. Kafin kafa kungiyar ya ce babu yadda Musulmi zai tashi ya je Sabuwar Tasha domin yana jin tsoro.Haka ma Kirista ba zai saki jiki ya je Rigasa ko Tudun Wada ba. To amma yanzu ana cudanya tare domin wanzar da zaman lafiya. Ya ce sun kai matsayin da ya kamata su godewa Allah domin sun cimma burinsu.

Daga birnin Zaria kuwa wasu masu jagorancin bikin Mauludin sun kara haske kan ranar. Malam Umaru Mai Jakar Karatu ya ce yau ranar farin ciki ce da babu iyaka sabo da so da suke yiwa manzon Allah. Ya ce mahimmancin ranar ita ce babu abun da Allah ya ba mutum da ya wuce manzonsa, wato Annabi Mohammed (S.W.A). Wannan ranar ita ce ta fi kowace rana mahimmanci a wurin Musulmi. Ranar babu irinta. Ranar farin ciki ce.

Ga karin bayani

XS
SM
MD
LG