Accessibility links

Musulmi a duk fadin duniya suna bukin karamar Sallah yau


Mata Musulmi suna sallar Idi a kasar Indonesiya
Yau Musulmi a duk fadin duniya suka gudanar da bukukuwan karamar Sallah bayan kamala azumin watan Ramadan.

Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewa, wadansu mahara sun bude wuta kan shingen jami’an tsaro dake kan titin Zariya dab da asibitin Aminu Kano, abinda ya haifar da musayar wuta tsakaninsu da rundunar tsaron.

Akwai sabanin rahotanni dangane da harin, inda mazauna unguwar suke cewa, maharan sun kashe jami’an tsaro biyu lokacin da suka bude wuta, yayinda rundunar tsaron ta musanta haka, sai dai kakakin rundunar yace an harbi wani dan sandan kwantar da tarzoma daya a kafa wanda aka dauka zuwa asibiti domin yi mashi jinya.

An dai gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da lumana karkashin tsauraran matakan tsaro sa sauran sassan Najeriya, bayan bayanan sirri da jami’an tsaro suka ce sun samu dake nuni da cewa, akwai yiwuwar kai hare hare lokutan bukukuwan sallah musamman a arewacin kasar. Wannan ya sa aka dage hawan Darba da aka saba gudanarwa ranar sallah a biranen Kano da kuma Maiduguri.
XS
SM
MD
LG