Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi A Fadin Duniya Sun Fara Azumin Ramadhan


Sallar Azumin bara, 2009 a MasallacinBaitul Ma'Mur Mosque dake gundumar Brooklyn, a birnin New York

Larabar nan al'ummar Musulmi a fadin duniya suka fara azumin watan Ramadhan, koda yake wasu 'yan mazhabin Shi'a za su fara azumin ne ranar alhamis

Musulmi a fadin duniya sun fara azumin watan Ramadhan, yayin da zafi mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya yake barazanar jefa masu yin azumin cikin karin wahala ta kishi.

An fara azumin da wuri a bana, koda yake akwai sabanin ra'ayi a tsakanin manyan mazhabobi biyu na Islama a kan ranar da ta dace a dauki azumin.

A yau laraba 'yan mazhabin Sunni suka fara azuminsu, yayin da ake sa ran 'yan mazhabin Shi'a zasu fara gobe alhamis. An samu wannan sabanin ne a dalilin bambanci wajen fassara lokaci da ranar tsayuwar wata.

Zafi mai yawan gaske da ake fama da shi a akasarin kasashen larabawa, ya haddasa damuwa ga wasu iyalai, musamman a wurare kamar Bagadaza da zirin Gaza inda aka saba dauke wutar lantarki na tsawon sa'o'i dama a rana.

Domin rage damuwar wadanda ala tilas su yi aikin kwadago da tsakar rana, manyan shaihunan malamai a Hadaddiyar Daular Larabawa sun fito da wata fatawa wadda ta kafa hujja ga leburori da su sha ruwa da wuri idan har zafi yayi tsananin da zai iya hallakawa ko galabaitar da su.

XS
SM
MD
LG