Accessibility links

Mutane 18 sun rasa rayukansu a wani harin da aka kai a Pakistan


Mutane suna kallon inda bom ya tarwatse a wata kasuwa
Jami’an tsaro a Pakistan sun ce harsasai masu linzamin da aka harba da jirgin Amurka da baya amfani da matuki ya kashe a kalla mutane 18 da ake kyautata zaton mayaka ne a arewa maso gabashin kasar, hari na biyar da aka kai a cikin mako guda.

Jami’ai sun ce an kai hari kan gidaje uku yau Jumma’a a yankin kabilu na Waziristan dake arewa, da ya kasance maboyar mayakan dake da alaka da kungiyar Taliban da kuma Al-qaida. Mutane da dama sun ji rauni a harin.

Wannan ne hari na biyar da aka kai tun daga ranar 18 ga watan Agusta, inda aka kashe mayaka 35 a Waziristan dake arewaci cikin mako guda da ya shige.

An kai harin na yau jumma’a ne kwana daya bayanda ministan harkokin kasashen ketare na kasar Pakistan ya gayyaci babban jami’in diplomasiyan Amurka domin bayyana rashin amincewarsu da hare haren, da ya bayyana a matsayin abinda ya sabawa dokar kasa da kasa da kuma keta diyaucin kasar Pakistan.
XS
SM
MD
LG