Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 25 Sun Mutu A Wani Harin Kunar Bakin Wake A Birnin Mogadishu


Wani ginin da ya ruguje bayan tashin bam din

A cigaba da bararraka birnin Mogadishu na kasar Somaliya da 'yan bindiga ke yi, jiya wani dan kunar bakin wake ya yi kundunbala ya kutsa da motarsa cikin cinkosan jama'a inda ya tarwatsa kansa ya hallaka mutane da dama.

An hallaka mutane a kalla 25 baya ga wasu 50 da su ka ji raunuka, a wani harin bam da aka kai da motar daukar kaya, daura da wani muhimmin shatale-talen da ke Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, a cewar jami’ai da kuma wasu ganau.

Tashin bam din, wanda ya auku daura da shatale-talen Zobe mai cike da hada-hada, da alamar wani dan kunar bakin wake ne ya haddasa, a cewar wani jami’in yansanda ga Muryar Amurka. Ganau sun ce bam din ya tashi ne yayin da hanya ta cinkushe.

Wani wakilin Muryar Amurka da ya je wurin ya kidaya gawarwaki akalla 25 yayin da ake jigilarsu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG