Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Na Arziki da Yin Fasakwaurin Bil Adama


John Kerry Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Rahoton shekara shekara da ma'akatar harkokin wajen Amurka ke fitarwa akan fatauci da fasakwaurin mutane ya nuna cewa lamarin ya zama ruwan dare gama gari

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce fasa kwaurin bil adama, na taimakawa kwarai wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, inda lamarin ya ke haifar da muzgunawa tare da wulkanta miliyoyin mutane, yayin da wasu ke zuba ido ana ayyukan lalata da cin zarafin bil adama a kusan duk kasashen duniya.

A rahoton da ta ke fitarwa a duk shekara, ma’aikatar ta bayyana wannan tsari a matsayin wani lamari na aikin bauta a zamanance, inda ake cin zarafin ‘yan mata da mata ta hanyar karuwanci, tare da tilastawa maza da mata da yara shiga ayyukan da ake biyan kudade kalilan, a wasu lokuta ma ba a biyansu.

Fasa kwaurin bil adama ba shi da iyaka a duk fadin duniya a cewar rahoton, kuma sana’ar ba ta la’akkari da dokoki.

Ana kuma samun hakan a wurare na ofisoshi da ma’aikatun kwadago da doka ta san da zaman su da kuma akasin hakan, wanda kuma hakan ka iya janyo illa ga bangarorin ma’aikata daban-daban da suka fito daga fannonin ilimi daban-daban.

XS
SM
MD
LG