Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 24 Suka Mutu A Rikicin Da Ya Ki Ci, Ya Ki Cinyewa A Kasar Thailand


Sojojin Thailand Zasu Tinkari 'Yan Zanga-zanga
Sojojin Thailand Zasu Tinkari 'Yan Zanga-zanga

Har yanzu ana yin fito-na-fito a tsakanin dakarun kasar Thailand da 'yan zanga-zangar kin jinin gwamnati a birnin Bangkok, inda mutane akalla 24 suka mutu a kwanakin da aka shafe ana yin ba-ta-kashi

Har yanzu sojojin kasar Thailand su na yin fito-na-fito da masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a Bangkok, inda mutane akalla 24 suka mutu a 'yan kwanakin da aka shafe ana gwabza fada.

Firayim minista Abhisit Vejjajiva ya fada cikin wani jawabin da yayi ta telebijin a cikin daren asabar cewa gwamnatinsa ba zata mika wuya ga 'yan zanga-zangar da ake kira "Masu Jajayen Riguna" ba. Mr. Abhisit ya ce shirin da gwamnati take yi shi ne na maido da kwanciyar hankali ba tare da "hasara sosai" ba, kuma ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma mutane dari daya da saba'in sun ji rauni tun lokacin da fada ya barke a babban birnin na Thailand a ranar alhamis. Akwai 'yan jarida da dama a cikin wadanda suka ji rauni.

Gwamnati ta bubbuga manyan kasidu ko Poster a turance wadanda suka ayyana unguwannin da 'yan zanga-zangar suka kame a tsakiyar birnin a zaman yankunan da za a bude wuta da harsasan gaske cikinsu. Sojoji su na bude wuta a kan 'yan zanga-zangar da harsasan gaskiya, yayin da 'yan zanga-zangar suke maida martani da bama-bamai hadin gida da kuma duwatsu.

Tun da fari a asabar din nan, 'yan Jajayen Riguna dake zanga-zangar sun kwace suka mamaye wata babbar mahadar hanyoyin mota dake bayan garin Bangkok.

XS
SM
MD
LG