Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin da Ya Kitsa Hari Mafi Muni a Tarihin Amurka Ya Zauna Otel-otel a Dakunan dake Kallon Filayen da Ake Shirya Shagulgula


Stephen Paddock mutumin da ya kashe mutane 59 tare da jikata wasu fiye da 500

Hukumomin tsaron Amurka sun gano cewa Stephen Paddock mutumin da ya kitsa hari mafi muni a tarihin Amurka ya zauna a dakunan otel otel dake kallon filayen da ake shirya shagulgula a Las Vegas da Chicago

Hukumomin tsaron Amurka sun ce Stephen Paddock – mutumin da ya kitsa hari mafi muni a tarihin Amurka a wannan zamani, ya zauna a wasu otel-otel da ke hangen wuraren da akan gudanar da shagulgulan waka a birnin na Las Vegas da kuma Chicago.

Rahotannin kafafen yada labarai da suka ruwaito jami’an tsaron kasar, sun ce Paddock ya kama dakuna biyu a wani otel a Chicago, wadanda daga cikinsu, za a iya hangen wajen wani bikin waka da ake yi a duk watan Agusta da ake kira Lollapalooza, wanda kuma yake samun halartar daruruwan mutane.

Sai dai bai shiga dakin ba, kuma babu masaniya ko yaje Birnin na Chicago a wannan karshen mako, kamar yadda kafar yada labarai ta TMZ ta ruwaito.

Baya ga haka, hukumomin Las Vegas sun ce, akwai dakunan da ya kama a wani gini da ke kallon wajen wani shagalin wake-wake da ake kira “Life is Beautiful Alternative Music Festival” kafin ya kai harin na ranar Lahadi.

Ma’aikatan otel din Mandalay Bay Resort, inda ya kama daki ya harbe mutane 58, sun ce Paddock ya nemi su bashi daki a can sama, wanda ke kallon wajen shagalin taron wake-waken da ya kai harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG