Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAFDAC Ta Gargadi 'Yan Najeriya Kan Amfani Da Jabun Riga Kafin COVID-19


Vaccine

Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta yi gargadi ga al’ummar Najeriya da su yi hattara wajen amfani da jabun magunguna ko allurar riga kafin cutar COVID-19 da ke yawo a fadin kasar.

Babbar daraktar hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Christiana Adeyeye ce ta bayyana haka a yayin wata zantawa da manema labarai ta kafar ZOOM a yanar gizo, inda ta ja hankalin cibiyoyin gwamnati da hukumomi da ma manya da kananan kamfanoni masu zaman kansu da su guji sayar da magani ko allurar riga kafin cutar COVID-19 da hukumar ba ta amince da ingancinsa ba, duba da cewa a yanzu ne ake kokarin tantance ingancin sabbin magunguana da allurai na riga kafin cutar da kuma dole ne a kula da lahani ko abubuwan da za su iya janyowa ga jikin bil’adama, don haka ba kowa ne zai yi amfani da su ba har sai hukumar ta ba da tabbacin haka, a cewar Mrs. Adeyeye.

Idan za a tuna kwamitin shugaban kasa da ke yaki kan cutar ta COVID-19 a kasar ya bayyana cewa Najeriya za ta amshikashin farko na allurar riga kafin cutar na kamfanin Pfizer da BioNTech wanda aka amince da shi, kana gwamantin tarayya za ta soma bai wa al’ummar kasar allurar riga kafin kafin karshen watan Maris.

Hakazalika kwamitin ya bayyana cewa a kashi na biyu Najeriya na sa ran karbar adadin allurar riga kafin cutar miliyan 42 a kyauta ta hanyar tallafi na COVAX da ke karkashin kulawa ta hadakar kasashe marasa karfi da ke neman riga kafin cutar a duniya wato Global Vaccines Alliance, lamarin da wani jami’i a hukumar fasa kwabri a kasar Aliyu Ibrahim Shira, ya ce gwamnati ce kadai ke da hakkin kawo riga kafin.

Tsohon shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriyya ta NCDC, Farfesa Abdulsalam Nasidi, ya bai wa 'yan Najeriya shawara da cewa kada wani da ke son kansa ya yarda a saida mashi maganin riga kafin COVID-19. Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya za ta bada riga kafin kyauta ba sai an biya kudi ba.

Daga karshe hukumar ta NAFDAC ta fadi cewa Najeriya za ta karba ta kuma bada allurar riga kafin cutar COVID-19 a kasar amma sai hukumar ta tantace ta kuma amince da ingancin allurar ga al’ummar kasar, wanda sai an bi matakan aiki wajen cimma nasarar hakan.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Shamsiyya Ibrahim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00


Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG