Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ba Zata Daukaka Kara Kan Bakassi Ba


Mutanen yankin Bakassi su na kamun kifi da almuru, a yankin mai arzikin mai a ranar 11 Agusta 2011
Mutanen yankin Bakassi su na kamun kifi da almuru, a yankin mai arzikin mai a ranar 11 Agusta 2011

Atoni-Janar na Najeriya, Mohammed Bello Adoke, yace maimakon haka zasu yi kokarin sayen yankin daga hannun kasar Kamaru.

Najeriya ta ce ba zata daukaka karar hukumcin da kotun duniya ta yanke na ba kasar Kamaru mallakin yankin nan na Bakassi mai arzikin man fetur da suka yi takaddama a kai ba.

Atoni-Janar kuma ministan shari'a na Najeriya, Mohammed Bello Adoke, ya fada yau talata cewa kasarsa ba zata kalubalanci hukumcin da kotun ta yanke a shekarar 2002 kan yankin Bakassi ba.

Adoke yace maimakon haka, watakila Najeriya ta yi kokarin sayen yankin daga hannun kasar Kamaru.

Gobe laraba 10 ga watan Oktoba ne wa'adin shekaru 10 na daukaka kara kan wannan hukumcin Kotun Duniya zai cika, saboda haka ne ma mazauna yankin na Bakassi dake daukar kansu a zaman 'yan Najeriya, suke kara matsa lamba kan gwamnatin Najeriya da ta daukaka kara.

Ana daukar yankin na Bakassi a zaman wuri mai tarin kifi, kuma ana kyautata zaton yana da dimbin arzikin man fetur da gas.

Najeriya ta mika ma kasar Kamaru ikon wannan yanki a shekarar 2008.
XS
SM
MD
LG