Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Nakasassu Sun Fusata da Yadda Hukumomi Suka Yi Watsi da Cibiyoyin Koyar Da Su


Makarantar Kurame dake Bassa a jihar Filato

A cewar nakasassu tsangwama da nuna wariya da ake yi masu a Najeriya suka sa basa jin dadin rayuwarsu duk da gudummawar da suke bayarwa wajen cigaban kasa.

A cewar nakasassu tsangwama da nuna wariya da ake yi masu a Najeriya suka sa basa jin dadin rayuwarsu duk da gudummawar da suke bayarwa wajen cigaban kasa.

Shugaban kungiyar "Beautiful Gate" dake tallafawa nakasassu, Ayuba Gofan, ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da tallafin naurorin kwamfuta da awaki da gyaran wani sashen makarantar kurame dake garin Bassa a jihar Filato.​

A cewar Ayuba Gofwen wanda shi ma nakasasshe ne gwamnati tayi watsi da cibiyoyin horas da nakasassu saboda haka ya bukaci hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu da su dinga kula da nakasassu.

Yayi misali da makarantar kuramen inda ya kai tallafi. Yace lokacin da suka kai ziyara kusan duka yaran a kasa suke kwana. Babu gadaje, babu taogogi a wasu dakunan kwana kuma basu da abinci. Babu azuzuwan karatu. Akan hada azuzu ukku ne wuri daya.

Yace ko a wuraren daukan ma'aikata ana nuna wa nakasassu gyama da wariya. Yace dalili ke nan da suke son ita makarantar ta dinga koyas da sana'o'in hannu ta yadda yaran da suka gama zasu iya dogaro da sana'ar da suka koya ba sai sun nemi aikin gwamnati ba.

Wani Abdullahi Roki Boy mazaunin garin Jos ya bayyana irin ukubar da nakasassu ke fuskanta. Yace yawancin wadanda suke da halin takarawa akan harkokin nakasassu basa yi saboda sau tari da sun ga nakasassun sai su dauke kai. Akwai nakasassun dake son zuwa makaranta amma basu da damar yin hakan. Makarantun nakasassun ma basu da inganci. Yace yakamata a ba nakasassu gudummawa sosai.

Shugaban kuramen dake Bassa John Gada ya bayyana matsalolin dake addabar makarantar da suka hada da rashin tsaro, rashin wuta, rashin abinci, da rashin gidajen malamai da makamantansu.

Madam Jummai Madaki tace lokaci ya wuce da al'umma zasu bar nawayar taimakawa nakasassu ma gwamnati kadai. Tace ba sai an tara kaya da yawa ba amma idan kowa na kawo abun da yake dashi zai taimaka ainun.

Kwamishaniyar harkokin mata da walwalar jama'a ta jihar Rufina Gurmiyen tace gwamnati zata cigaba da inganta rayuwar nakasassun jihar.

Makarantar kuramen da aka kafa fiye da shekaru arba'in ita ce cibiyar horas da kurame ta farko a Afirka ta Yamma.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG