Accessibility links

Najeriya ta kaddamar da gangamin hana shan taba sigari kamar yadd MDD kebe


sigari

Juma'a 31 ga watan mayu, rana ce da MDD ta kebe domin gangamin hana shan taba sigari, hukumar kula da lafiya ta MDD tayi kira ga kasa da kasa da su kokarta ganin ba'a yi tallan taba sigari ta kowace kafar sadrwa ba, ko daukan nauyin tallan taba sigari ta wat siga ta dabam. Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a minna, cibiyar jihar neja ya aiko da wannan rahoton.

A wannan rana ta 31 ga watan Nayu ne MDD ta ware domin yin tuni ga irin illar da shan taba sigari ke yiwa Dan Adam.Hukumomi a matakai dabam-dabam na fadarkwa ga jama’a domin nuna irin illar da taba sigari ke yiwa mutane.

Hukumomin lafiya sun bayyana cewa kimamin mutane miliyan 93 ne ke zukar taba sigari a Nigeria. Dokta Muhammad Usman, jami’in kiwon lafitya ne a jihar Neja Nigeria, yayi cikakken bayani game da illar shan taba sigari a tattaunawarsa da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari.

Wakiln sashen Hausa na Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad, ya tattauna da masu shan taba sigari a jihar Bauchin Nigeria kan matsalar da masu shan taba Sigari ke fuskanata, musamman game da lafiyarsu. Sannan ya aiko da cikakken rahoto daga Bauchi, Nigeria.


XS
SM
MD
LG