Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NATO Zata Bukaci Kasashen Kungiyar Su Kara Mata Kudi


Sakataren NATO-Jenar Jens Stoltenberg

Babban sakataren kungyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya fada jiya Talata cewa, taron da ministocin tsaro da suke cikin kungiyar zasu yi zai maida hankali ne kan bukatar kasashe da suke cikin kungiyar su kara kudade da suke kashewa kan harkokin tsaro.

Ya gayawa manema Labarai a Brussels, gabannin taron kungiyar cewa, kasashe sun kara kudade da suke kashewa kan tsaro da dala bilyan 10, a bara, amma kasashe biyar biyar ne kadai cikin kasashe 28 dake kungiyar da suka ware kashi biyu cikin tattalin arzikin kasarsu domin tsaro.

Shugaban Amurka Donald Trump lokacin yakin neman zabe ya soki kasashe da suke cikin kungiyar ta NATO cewa, kalilan ne suke taimaka mata da kudi. Har ma yace Amurka ba zata kare kasashen da suka kasa biyan hakkokinsu ba.

Amma Stoltenberg ya lura cewa, tun bayan da ya kama aiki, shugaba Trump yana bayyana goyon baya ga kungiyar, a zahiri da kuma a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho sau biyu.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG