Accessibility links

Nijar Da Burkina Faso Sun Musanta Suna Kokarin Baiwa Gadhafi Mafaka

  • Aliyu Imam

Wani mai goyon bayan kanal Gadhafi yake rike da hotonsa a wata zanga-zanga da aka yi a birnin Moscow na nuna goyon baya gareshi.

An sami rahotanni dake cea gwamnatocin jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, sun musanta labari da ake yayatawa cewa suna kokarin baiwa hambararren shugaban Libya kanal Gadhafi mafaka.

An sami rahotanni dake cewa gwamnatocin jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, sun musanta labarin da ake yayatawa cewa suna kokarin baiwa hambararren shugaban Libya Moammar Gadhafi mafaka.

Mutuminda shugabannin gwamnatin rikon Libyan suka sake jaddada niyyarsu ta gurfanar dashi gaban shari'a.

Ministan shari'a na jamhuriyar Nijer Marou Amadou, Gadhafi baya jamhuriyar Nijer, kuma a matsyinsa shi Gadhafi na tsohon shugaban kasa, da wuya ya shiga wata kasa ba tare da an sanar da shugabanninta ba.

A gefe daya kuma duk da cewa makonni biyun d a suka wuce kasar Burkina Faso ta bada sanarwar baiwa Gadhafi mafaka,amma ya zuwa yanzu bai karbi tayin ba, don haka Gadhafi bai shiga kasar ba. Wani mai magana d a yawun gwamnatin kasar, yayi karin hasken cewa gwanatin Burkina Faso ta janye ta janye tayin da ya yi Gadhafi.

Burkina Faso da Nijar tuni suka amince da kafuwar gwamnatin rikon Libya. Sai dai Gadhafi yana ci gaba da samun goyon baya da farin jini daga al'umar nahiyar Sahel, musamman kasashe dake makwabtaka da Libya.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG