Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Yasa Nijar Ta Karawa Kananan Hukumomi Wa'adi, Amma Banda Birnin Niamey?


NIGER: Shugaba Isouffe a wani bikin kaddamar da wani asibiti.

Majalisar ministocin kasar ce ta amince da karin wasu wata shidan, bayan da gwamnati ta kasa gudanar da zaben kananan hukumomi.

Shekara daya bayan da ta kasa gudanar zaben kananan hukumomi a duk fadin kasar, gwamnatin Nijar ta shugaba Muhamadu Isouffu, ta kara wa’adin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a duk fadin kasar.

Amma wannan karin wa’adi na wata shida, bai shafi karamar hukumar Niamey ba.

Gwamnatin kasar bata bada dalilin tsame da’irar Niamey daga wannan shiri na karin wa’adin ba, abunda ya dami ‘yan hamayya kamar Tahir Gimba na jam’iyyar Modem Ma’aikata. Yace akwai bukatar matakin ya shafi kowa muddin ana son kawo hadin kai da ci gaba a kasar. Yace kowa ya san cewa Niamey yana hanun jam’iyyar Lumana, yanzu sun zura ido su ga wa za’a nada domin iko kan yankin.

Masu rajin kare demokuradiyya, irin su Lawwali Adamu, cewa ya yi wannan mataki ya kaucewa tsarin demokurdiyya, kuma akwai bukatar dukka ‘yan kasa su tashi haikan domin yaki da wannan tsari.

Wani masanin tsarin mulkin kasar Bubakar Amadou Hassan ya gayawa wakilin Sashen Hausa Sule Barma cewa da an sami ganin dokar sauye sauyen ne da watakila zai taimaka wajen gane ko matakin yana da nasaba da zargin rashin tsabta da shugaba Muhammadu Isouffe ya yi akan shugaannin birnin, har ta kai ga cire shugaban karamar hukumar makoni biyu da suka wuce.

Wannan sabon wa’adi zai fara aiki ne daga Laraba 16 ga watan nan na Agusta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG