Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJER: Za A Fara Ayyukan Yaki Da Wutar Daji Da Bunkasa Tattalin Arziki


Yayin da hukumomin gandun daji suka kaddamar da fara aikin yaki da wutar daji, duba da lokaci ne da iska ta fara kadawa kuma aka fi samun gobara, kimanin kilomita dubu goma sha daya ne za a kare a cikin kasa inda za a kashe kudade har miliyan dari biyar da saba'in na cfa

Kanal Almajir Mamman Badamasi, shine daraktan hukumar gandun daji ta jihar Damagaran, ya bayyana cewa a yunkurin kokarta are wutar daji gwamnatin kasar ta bada sanarwar da zarar an kammala ruwan sama na damina, a fada gudanar da ayyukan.

Daraktan ya bayyana cewa a jihar Damagaran kadai, gwamnati zata debi kusan kilomita dubu, bayan haka kuma, akwai masu hannu da shuni da suke tallafawa gwamnati da kuma wata kungiya da itama zata dauki dawainiyar kusan kilomita dari takwas.

Ayyukan sun hada da saka shingaye wadda wata hanya ce ta samar da abincin dabbobi, domin duk kilomita guda zata kare sama da kadada talatin a cewar daraktan, dan haka koda wutar ta kama idan ta kai inda aka shinge, ko aka nome hakin dake wurin, bazata ci gaba da ci ba.

Muhimmancin awannan aiki da za a fara gudanarwa zai taimaka wajan taimakawa matasa rage yawan tafiye tafiye, dan haka a cewar Almaji, wata sabuwar hanya ce da zata taimakawa tattalin arzikin kasa.

Saurari rahoton Tamar Abari a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG