Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ma Ta Takaita Zirga-zirgar Jami'an Amurka.


Jami'an tsaro ke gadin kofar shiga ofishin jakadancin ofishin jakadancin Amurka a Lahore.

Wannan mataki ya biyo bayan irin wannan umarni da Amurka ta bayar kan jami'an difilomasiyyar Pakistan cewa sai sun sami izinin idan zasu yi tafiya wacce ta dara kimita 40.

A wani mataki na ramuwar gayya, Pakistan ta bada sanarwar takaita zirga zirgan jami'an difilomsiyyar Amurka a kasar, kuma ta janye dukkan wani sassauci data yiwa ofisoshin jakadancin Amurka, a zaman wani bangare na "yaki da ta'addanci," mataki da ya kara jefa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin wani mawuyacin hali.

Wannan mataki da Pakistan ta dauka ya biyo bayan umarni da hukumomi a Washington suka bayar cewa, jami'an difilomasiyyar Pakistan a Amurka su nemi izini kwanaki biyar idan zasu yi balaguro da ya zarce kilomita 40 daga wurin aikin su.

Pakistan ta tabbatar da cewa matakin na Amurka kan jami'an difilomasiyyarta ya fara aiki daga jiya jumma'a 11 ga watan nan na Mayu.

Dangantaka tsakanin Amurka da Pakistan ta tabarbare tun lokacinda gwamnatin Trump ta kama aiki, bayan da shugaban na Amurka ya bada sanarwa kan sabbin matakai a yankin kudancin Asia, inda ya zargi Pakistan cewa tana goyon bayan kungiyoyin ta'addanci a fakaice ciki harda Taliban.

Jami'an Pakistan sun musanta wannan zargi, suna cewa hukumomin Amurka suna fakewa da gazawar su a Afghanistan su aibanta Islamabad.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG