Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka Janar Petreaus Yayi Murabus...


View of South America and portions of North America and Africa from the Mercury Dual Imaging System’s wide-angle camera aboard MESSENGER (Mercury Surface, Space Environment, Geochemistry, and Ranging). (Credit: NASA/Johns Hopkins University Applied Physics Laboratory/Carnegie Institution of Washington)
View of South America and portions of North America and Africa from the Mercury Dual Imaging System’s wide-angle camera aboard MESSENGER (Mercury Surface, Space Environment, Geochemistry, and Ranging). (Credit: NASA/Johns Hopkins University Applied Physics Laboratory/Carnegie Institution of Washington)
Janar David Petreaus mai ritaya, mutuminda ake jijinawa wajen nasarar karkato yakin Amurka a Iraqi, yayi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar leken asiri na Amurka watau CIA, sabo da zina.
Janar David Petreaus mai ritaya
Janar David Petreaus mai ritaya

A cikin wasika da ya rubutawa ma’aikatan hukumar CIA, Petreaus ya gaya musu cewa shi da kansa ya mikawa shugaba Obama takardarsa neman ajiye aiki ranar Alhamis. Ya kara da cewa shi Petreaus ya yi ragwan tunani” kuma wannan ba hali ne da ya dace da mutuminda ya kasance shugaba ba.

Tsohon janar na mayakan Amurkan, yace babban karamci ne a gareshi na aiki a hukumar CIA, daga nan ya godewa ma’aikatan hukumar saboda aiki tukuru da suke yi.
Shugaba Obama yace ta aikinda janar Petreaus yayi dokacin rayuwarsa a soja da kuma kasancewa shugaban hukumar leken asiri ta Amurka, ya kiyaye lafiyar Amurka, kuma ya kara karfafata.

Kafofin yada labaran a Amurka sun bada rahoton cewa hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI ce ta bankado lalatar da janar din yake yi, lokacinda take binciken wata ‘yar jarida Paula Broadwell, saboda tana kokarin samun bayanan sirri ta kafar email din janar Petreaus. ‘yar jaridar ta rubuta littafi kan tarihin rayuwar janar Petreaus, kuma rahotannin sun ce bata da shamaki zuwa gun janar Petreaus a lokacinda yake Afghanistan.

Amma ita hukumar FBI bata ambaci Paula Broadwell cewa itace matar da janar din yake lalata da ita ba, shi ma janar Petreaus bai bayyana sunan matar ba.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG