Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin 'Yan Nijar Kan Dan Takarar Shugaban Kasar Faransa Fillon da Ya Fada Wata Badakala


Dan takarar shugabancin kasar Faransa Francois Fillon wanda wata badakala ta mamayeshi

Francois Fillon wanda dan majalisa ne ya fito yana neman shugabancin kasar Faransa kuma har yana kan gaban duk sauran 'yan takaran kafin a gano cewa lokacin da yake majalisa ya kwashi shekaru 15 yana biyan matarsa albashi na maho da kudin majalisar alhali kuwa bata yi aikin komi ba

A zaben fidda gwani na jam'iyyarsa Francois Fillon ya kada wani tsohon shugaban kasa, ya kada manyan 'yan siyasa da gaggan wadanda ake kyautata zaton ba zai iya karawa dasu ba domin masu ra'ayin rikau ne kamarsa.

Wadannan mutanen da ya kadasu sun amince da shan kaye daga wurinsa amma basu razana ba. Su ne suka koma gefe daya suka kama tone-tone har suka ci karo da badakalar da yanzu ta zama wa Farancois Fillon alakakai.

Tunda Francois Fillon ya samu wannan tabon da wuya ya tsira har ya kaiga nasara saboda su turawa duk lokacin da aka sameka da rashin gaskiya to da wuya ka kai labari gida. Abun da ya faru ya riga ya rage masa farin jini ainun wurin jama'ar kasar.

Da maganar ta fara fitowa Francois Fillon yace kuskure yayi ya kuma nemi gafara amma mahukumta suka ce dole a binciki lamarin. Sakamakon binciken kuma ya kara masa muni.

Abun da ya faru yanzu da wuya jam'iyyar Francois Fillon ta samu shugabancin kasar domin ko an maye gurbinsa da wani babu lokacin cimma sauran 'yan takarar.

Dangane da 'yar takara mace daya tilo Marine Le Pen ana ganin ba zata ci zabe ba domin Faransawa basa zaben mace shugaban kasa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG