Accessibility links

Rahoto na Musamman Kan Nelson Mandela


Takardar kudin Afirka Ta Kudu da hoton Nelson Mandela

Bayan an binne tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela an soma duba tarihin marigayin a wannan rahoto na musamman.

Shugaba Nelson Mandela wanda ya yi shekaru casa'in da biyar a duniya an haifeshi ne ranar 18 ga watan Juli a shekarar 1918 a cikin kabilar Timbu.

A shekarar 1925 ne Nelson Mandela ya fara karatunsa na firamare kuma malaminsa ya sa masa suna Nelson biyo bayan kasa rashin iya fadar sunansa na ainihi. Bayan ya kammala karatunsa na firamare ya fara karatun sakandare a shekarar 1937. A shekarar 1939 ne ya fara karatun jami'a. Daga wannan lokacin ne ya fito fili ya nuna fafitikarsa da wariyar launin fata da 'yanuwabsa bakake ke fuskanta a kasar a hannun fararen fata.

A jami'a ce a shekarar 1940 a ka koreshi biyo bayan shigewa sawun gaba da yin zanga-zanga. Ya shiga birnin Jahannesburg a shekarar 1941inda ya soma aikin mai gadi a wani kamfanin ma'adanai kuma a wannan shekarar ce suka hadu da Walter Sisulu wanda ya sa a ka dauke shi aiki a matsayin akawun wata kamfanin lauyoyi mai zaman kansa.

Haduwarsa da Walter ya sa sun zama abokan kud-da-kud domin shi Walter yana cikin kungiyar ANC kuma ita ce babbar kungiya mai yaki da wariyar fata a wannan lokacin.

A shekarar 1942 ne Nelson Mandela ya fara halartar taron kungiyar kuma a lokacin ne ya fara karatun jami'a amma ba na zama cikin jami'a ba. Yana wannan karatun ne suka hada kungiyar matasa ta ANC tare da Walter Sisulu da Oliver Tambo kuma suka fito fili suka bayyana matakan cigaba da yaki da wariyar launi.

A shekarar 1948 a ka zabeshi sakataren kungiyar ANC amma bangaren matasa. A wannan shekarar ce Nelson Manadela ya fara jan daga na garin da garin da turawa masu nuna ban-bancin wariyar fata. A shekarar ce ya jagoranci zanga-zangar kin jinin gwamnati mai nuna wariyar fata. Daga bisa ni an kamashi da Walte Sisulu a ka yi masu dauri mai tsanani. To sai dai yana fitowa sai ya zama kamar an kara masa kaimi ne. Ya ce domin fafitika lokacin ne ya fara shi kain-da -nain.

Kafin a farga sunan Nelson Mandela ya bazu a duk fadin kasar Ta Afirka Ta Kudu musamman a cikin bakake. Wannan ya sa turawa suka kara kafa dokoki masu tsananin gaske a kan mulkin kasar. Daga bisani Nelson Mandela ya fada hannun hukuma ranar 12 ga watan Yuni a shekarar 1964.

Kafin a samu a kama shi an sha gwagwarmaya da shi, ya boye na ko ya boye can. Daga baya dai sun kama shi sun garkame.

Sai dai shugaba P. W. Botta ya yi yunkurin sakeshi a shekara 1985 amma fa da sharadin ba zai cigaba da fafitika ba. Nelson ya ce ina anfanin 'yanci ba walwala kuma ina a ka taba jin an yi sulhu da dan gidan yari. Ya ce da mai 'yanci ake sulhu. Idan za'a sakeshi kuma yana kallo ana gallazawa bakaken fata ukuba to baya so. Haka ko aka yi ya cigaba da zama gidan kaso.

A shekarar 1990 shugaba De Ckark ya saki Nelson Mandela ba tare da shimfida masa wasu sharruda ba. Yana fitowa ya ce ya yafewa wadanda suka tsareshi a gidan kaso.

Yayin da yake kamfen neman zabe ya ce sun jajirce ne yin yaki da wariyar launi domin duk mutum, mutum ne. Ya ce fafitikarsu ta sa babake sun gane abun da suka yi.

Halayen da ya nuna sun sa yau fararen fata na kan gaban masu yabonsa har zuwa lokacin da ya rasu.

Ga cikkaken rahoto.

XS
SM
MD
LG