Accessibility links

Rai Ya Salwanta Sanadiyar Zanga-Zangar Daliban Jamhuriyar Niger


Shugaba Mouhammadou Issouffou, Junhuriyar Nijer

Daliban makarantar share faggen shiga jami'a sun tada bori da zanga-zanga domin rashin kayan aiki wanda har ya kai ga asarar rai.

Daruruwan dalibai dake karatu a makarantun share faggen shiga jami'a sun fantsama cikin zanga-zanga da yiwa gwamnati Jamhuriyar Niger bori bisa ga wasu dalilai.

Daliban sun shiga zanga-zangar ce ta nuna rashin jin dadinsu da abubuwan dake faruwa a makarantunsu. Suna fuskantar matsalolin rashin azuzuwan daukan karatu. Babu wadatattun malaman karatun boko. Bugu da kari babu ma isassun kujerun zama wanda ya sa wasu da yawa a tsaye suke daukan darutsa. Sun yi wannan borin ne a birnin Niamey babban birnin Jamhuriyar Niger.

Zanga-zangar ta zama irinta na farko bayan da dalibai suka koma makarantunsu a duk fadin kasar. Uwar kungiyar daliban ta kara haske kan matsalolin da dalibai ke fuskanta a makarantunsu. Malam Nuhu Haruna mataimakin magatakardan kungiyar dalibai na kasa ya ce a duk fadin kasar watakila za'a samu makarantu hamsin da basu da matsalar runfunan karatu. Amma har kawo lokacin wannan rahoton akwai wasu makarantu uku da basu da wurin da dalibai zasu zauna. Ya ce wannan matsala ce da gwamnati zata iya magancewa domin lamarin bai taka kara ya karya ba.

Wakilin Muryar Amurka a Niamey ya yi tattaki zuwa ofishin gwamnati mai kula da ilimin gaba da sakandare inda ya tattauna da daraktan ma'aikatar domin jin ra'ayin gwamnati dangane da zanga zangar da daliban suka shiga. Ya yi batun ba daliban zana idan damina ta kare. Don haka inji shi sai su jira.

Zanga-zangar da ta sa daliban sun yi kone-kone da fashe-fashe lamarin da ya sa jami'an tsaro suka cafke wasu daga cikin daliban. Cikin gwagwarmayar da jami'an tsaro har wani dalibi ya samu rauni ya mutu. Malam Nuhu Haruna ya ce jami'an tsaro sun kama abokansu kuma sun tsaresu. Ya ce wasu da dama sun ji rauni har ma daya ya mutu. Sabili da haka yanzu ne ma suka fara yaki da gwamnati.

To sai dai bangarorin gwamnati da na daliban suna kan teburin shawara domin samo bakin zaren warware takaddamar. Daliban sun ce idan ba'a samu masalaha ba zasu kwashe kwanaki uku suna kauracewa makarantunsu da kuma cigaba da bori kala-kala har sai sun ga abun da ya ture ma buzu nadi.

Abdullahi Maman Ahmadu nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG