Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar tunawa da kafa mulkin dimokradiya a Najeriya, wato ranar da sojoji suka mika ragamar mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula


Wata mace na kada kuri'a a lokacin zabe a Najeriya, wasu kuma suna layi domin su jefa nasu kuri'un.
Wata mace na kada kuri'a a lokacin zabe a Najeriya, wasu kuma suna layi domin su jefa nasu kuri'un.

Ranar ashirin da tara ta kowane watan Mayu rana ce da Najeriya ke bikin kafa dimokradiya a kasar.

Ranar ashirin da tara ta kowane watan Mayu rana ce da Najeriya ke bikin kafa dimokradiya a kasar. Ranar ta samo asali ne daga Mayu 29 na shekarar 1999 ranar da Janaral Abdulsalami ya mika wa Chief Obasanjo wanda aka zaba ta hanyar dimokradiya ragamar mulkin Najeriya. Sai dai a ranar Mayu 29 shekarar 2010 yan tsageran Neja Delta sun kai harin kunar bakin wake kusa da dandalin dimokradiya inda ake tunawa da ranar. Lamarin ya sa tun daga lokacin gwamnatin Najeriya ta dena bikin ranar a bainar jama’a.

Yayin da ake tunawa da ranar a wannan shekarar wasu basu yarda Najeriya na bin tafarkin dimokradiya karkashin mulkin jam’iyyar PDP ba balantana a ce an ci gajiyarta. Tabarbarewar tsaro a kasar ya shafi harkokin rayuwa dama na komai a kasar.

Nasiru Adamu El-Hikaya na da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG