Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ma Ta Kakabawa Amurka Takunkumi


Shugaban Rasha Vladimir Putin

Bayan da Amurka ta kakabawa Rasha da wasu jami'anta takunkumi, ita ma Rasha ta mayar da martani ta kakabawa Amurkan takunkumi

‘Yan Majalisar Dokokin kasar Rasha, jiya Talata, da gagarumin rinjaye su ka amince, bayan karatu na farko, da dokar kakaba takunkumin ramuwar gayya kan Amurka da wasu kasashen Yamma saboda wasu takunkuman da Amurka ta kakaba ma wasu manyan kamfanonin Rasha da manyan ‘yan kasuwan Rasha.

Wani bangare na dokar zai bai wa fadar Shugaban kasar ta Rasha ikon kakaba takunkumin ramuwar gayya ta kowace hanya. Wani sashin dokar kuma ya haramta mutunta takunkumin da Amurka ta kakaba ma Rasha ko kuma bayar da wani bayani ko shawara kan yadda za a hukunta wanda bai kiyaye ba.

Hukuncin kin yin huldar kasuwanci da attajiran Rasha da kuma kamfanomnin da Amurka ta kaka ma takunkumi zai hada da kurkukun shekaru 4.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG