Accessibility links

Rick Santorum Ya Lashe Zaben Fidda Dan Takara A Jihohi Biyu Dake Kudu.

  • Aliyu Imam

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Rick Santorum.

Rick Santorum ya lashe zaben ‘yan takara na jam’iyyar Republican da aka yi jiya talata a jihohin Alabama da Mississippi, dake kudancin Amurka.

Rick Santorum ya lashe zaben ‘yan takara na jam’iyyar Republican da aka yi jiya talata a jihohin Alabama da Mississippi, dake kudancin Amurka, da wan nan nasara ya sake jaddada matsayarsa cewa shine dan takara mai ra’ayin mazan jiya na tsantsa, wani zabi baya ga Mitt Romney, mutumind a yake kan gaba a zaben.

Santorum ya sami nasara amma ba da gagarumin rinjaye ba a jihohin da mazauna can masu ra’ayin rikau ne sosai, Gingrich ne yazo na biyu, shi kuma Romney yazo na uku.Tsohon senata daga jihar Pensylvania ya gayawa magoya bayansa cewa “a yakin neman zabensa yana maida hankali ne kan talakawa, wadanda suke nuna bajinta” ya kara da cewa saboda sune yake ci gaba da bada mamaki.

Yace lokaci yayi da masu ra’ayin mazan jiya zasu hade wuri daya, domin su tunkari shugaba Barack Obama dan Democrat a zaben kasa da za’a yi cikin watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG