Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Ya Sake Barkewa Tsakanin Yahudawa da Falasdinawa


Wata tsohuwa 'yar shekaru 80 da haihuwa da wani Bafalasdine ya soka da wuka ana kaita asibiti

Bayan an dan samu sauki sai gashi jiya Litinin Yahudawa da Falasdina sun kuma shiga suka da wuka da kuma harbi da bindiga

Jiya Litinin an kaiwa Yahudawa hudu hari yayinda aka sokesu da wuka. Wadanda aka kaiwa hari sun hada da wani dan shekara 70 da haihuwa wanda ya samu mugun rauni a arewacin birnin Netantaya dake gabar teku yayinda 'yansanda suka kashe Bafalasdinu dan shekara 22 wanda ya soki mutumin.

Mahukuntan Israila sun ce shi dan shekara 22 din da ya soki mutumin mai shekaru 70 daga garin Tuikam ya fito na yankin West Bank.. Nan take 'yansanda suka bude wa matashin wuta ya kuma rasa ransa tare da hanashi kaiwa wani hari kuma.

'Yansanda sun ce lamarin ya auku ne sao'i kadan bayan da wani Bafalasdine ya soki mutane da yawa da wuka da suka hada da wata tsohuwa 'yar shekara 80 kusa da birnin Tel Aviv. Harin jiyan shi ne aka samu cikin wata daya da kura ta lafa.

Kawo yanzu rikicin ya rutsa da Yahudawa 11 a harin suka da wuka da Falasdinawa suke kaiwa. A nasu bangaren kuma Falasdinawa 69 ne jami'an tsaron Israila suka harbe da suka hada da mutane 43 da Yahudawa suka ce suna cikin wadanda suka kai hari ko kuma suna kokarin kai hari

XS
SM
MD
LG