Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Gwabza Rikicin Kabilanci A Kyrgyzstan


Wani dan kabilar Uzbek ya rike kai yana kuka a kofar gidansa da aka kona kurmus a birnin Osh, litinin 14 Yuni 2010.

Yayin da ake ci gaba da jin karar harbe-harbe, jami'ai sun ce an kashe mutane akalla 124, wasu fiye da dubu daya da dari shida suka ji rauni a wannan yamutsin da aka fara tun ranar alhamis.

An ji karar harbe-harbe litinin a biranen kudancin Kyrgyzstan, a rana ta hudu ta rikicin kabilancin da ya tilasta ma 'yan kabilar Uzbek kusan dubu 100 suka gudu daga gidajensu, suka taru kusa da bakin iyakar kasar da Uzbekistan.

Jami'ai sun ce an kashe mutane akalla 124, wasu su fiye da dubu daya da 600 suka ji rauni a wannan rikicin da ya faro tun ranar alhamis. Shugabannin al'ummar Uzbek sun ce adadin mutanen da suka mutu sun fi haka.

A yau litinin, shaidu sun ce gungu-gungun mazaje dauke da makamai su na yawo a kan titunan birnin Osh, haka kuma an samu rahoton yin arangama a birnin Jalalabad a kudancin kasar. An ce 'yan kabilar Kyrgyz sun kona gidaje da kantuna a unguwannin 'yan kabilar Uzbek, inda har wasu 'yan kabilar Kyrgyz suke ikirarin cewa su na kare kudancin kasar ne daga yunkurin da 'yan Uzbek ke yi na kwace shi.

Gwamnatin rikon-kwarya ta Kyrgyzstan ta ce zata tura sojojin wucin-gadi zuwa wannan yanki inda tsohon shugaba Kurmanbek Bakiyev, yake da karfi. An hambarar da gwamnatinsa a boren da ya kashe mutane 85 ranar 7 ga watan Afrilu. Hambararren shugaban, wanda ya nemi mafaka a kasar Belarus, ya musanta zargin da shugabannin rikon-kwarya suka yi cewa magoya bayansa ne suke rura wutar wannan rikicin kabilanci.

Ba a dai san wanda ya tayar da fitinar ba, amma a yau litinin, jami'an gwamnatin rikon kwarya sun ce sun kama wani sanannen mutum bisa zargin tayar da wannan hargitsi.

An kafa sansanoni ma 'yan gudun hijira a cikin kasar Uzbekistan mai makwabtaka da nan. Kungiyoyi na kasa da kasa su na aikewa da magunguna da wasu kayan na agaji zuwa yankin kudancin Kyrgyzstan.

XS
SM
MD
LG