Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Anambra Ta Shirya ta Tabbabatar da Tsaro Lokacin Sallah


M.D Abubakar, Sefeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya

Lamarin samar da tsaro a Najeriya ya zama babban kalubale a wasu sassan kasar amma a jihar Anambra rundunar 'yansandan tace zata tabbatar da tsaro lokacin sallah

Usman A Gwari shi ne kwamishanan rundunar 'yansandan jihar Anambra kuma ya tabbatar da samar da ingantacen tsaro a lokacin bukuwan sallah.

Yace kamar yadda aka saba rundunar 'yansandan jihar ta shirya tsaf domin tabbatar cewa an gudanar da bukukuwan karamar sallah cikin lumana da kwanciyar hankali a duk fadin jihar. Yace ya tanadi 'yansandan da zasu kasance a wuraren ibada kamar su idi da wuraren da yara da mutane zasu je suna hidimomin sallah.

Su ma 'yan asalin arewacin Najeriya dake zaune a yankin sun bayyana ra'ayoyinsu akan bikin sallar. Yusuf Suleiman Galadima yace lamarin da sallah ta fada ciki ta kawo matsala da tagayyara domin mutane yanzu ba maganar sallah suke yi ba maganar zaman lafiya ya damesu. Yace suna zaune shiru babu wanda zai san ana ma shirin sallah. Irin tafiye tafiyen da aka saba yi ya gagara bana. Jami'an tsaro suna kokari domin duk lokacin sallah sukan bada tsaro sosai. Bana ma yace suna fata a yi a tashi lafiya.

Hajiya Asabe tace sallar ta zo amma babu kudi saidai suna fatan zasu iya fita su ga abokan arziki. Tayi fatan jami'an tsaro zasu kula dasu domin su yi sallah lafiya.

Daga bisani dai jama'a sun yiwa Allah godiya domin suna cikin koshin lafiya kuma wadanda suke zaune dasu da ba musulmi ba suna yi masu fatan alheri. Amma sabili da halin rashin kudi zasu yi sallah daidai gwargwadon abun da suke dashi.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG