Accessibility links

Gwamnatin Legas tana rushe gidajen masu karamin karfi dake bayan gari domin wai an ginasu ba kan kaida ba kuma da izinin hukumar birnin Legas ba.

Birinin Legas na cigaba da rushe gidajen marasa karfi dake bayan birnin sabili da wai ba'a ginasu bisa ga kaida ba ko izinin hukumar birnin, Gidanjen an ce basu da tabbacin kiyaye lafiyar mutanen. A madadinsu za'a gina ingantattu kuma masu rahusa da talaka zai iya saya.

Domin gano ko menene musabbabin rushe gidajen abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta da dan rajin kare hakkin bil adama, Alhaji Aminu Sule, kan dokokin gine-gine da mallakar muhalli. Ya ce duk abun da gwamnati ko hukuma zata yi a Najeriya dole akwai dokoki da suka yadda da yin hakan. Dole ne ana da tsari na yadda za'a aiwatar da komi. Sai dai wani zubin gwamnati ta kan yi wasu abubuwa ba tare da la'akari ko talaka ya fahimci manufofinta ba. Batun rushe gidaje abun da gwamnati ke yi nada fuskoki daban. Wasu gidajen ruwa na iya cinyesu. Wasu kuma na gwamnatin tarayya ne. Ya ce bisa ga dokar kasar duk filaye na hannun gwamnati, wato mallakar gwamnati ne. Idan gwamnati tana bukatar wani wuri sai ta duba ko wadanda ke zaune a wurin suna da takardar mallaka ko a'a. Gwamnati zata biya diyya ne bisa ga irin takardar mallaka da na izinin gini da mutum ke dashi.

Game da korafe-korafe da mutane ke yi a Legas cewa ana rushe masu gidaje ba bisa kaida ba sai ya ce duk duniya ta yarda cewa ruwa na cin gidaje a Legas. Wanna abu babban illa ne kuma ga karanci kasa sosai. Bugu da kari ga kuma yawan jama'a. Wadannan su ne suka haddasa matsaloli da dama da suka sa gwamnan jihar na yanzu yana son ya yi maganinsu. Yawan ambaliyan ruwa ya kawo matsala kuma yawancin gine-ginen ba bisa kaida suke ba. Wadannan matsalolin sun sa ya zama dole a yi tunane tsakanin gwamnati da jama'a domin samun mafita.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG