Accessibility links

Sabon Shugaban Kasar Iran Yayi Magana


Zababben Shugaban Iran Hassan Rohani yana daga manema labarai hannu a ganawa da yi da su a birnin Tehran ran 17 ga watan Yunin 2013.

Sabon zababben shugaban kasar Iran Hassan Rouhani na kira da a ringa yin amfani da tattaunawa mai hikima wajen warware matsalolin duniya kamar yake-yake da ta’addanci.

A wani sharhi da ya rubuta a jaridar The Washington Post, Mr. Rouhani yace hanyoyi masu hikima ba dole sai sun kwace wa mutum ‘yancinsa ba. Yace hakan na nufin hawa teburin fahimtar juna domin cimma buri iri daya, da kuma warware matsalolin dake addabar juna.

Yace ta tattauna, bangarori biyu zasu iya yin nasara. Yace tsayawa akan turba daya ba tare da fahimtar daya bangaren ba, na hana tasirin tattaunawa mai hikima.

Shugaban Iran din ya rubuta cewa siyasar kasa da kasa, ba abu ne kara zube ba, amma wani fagge ne mai fuska daban-daban inda hadin kai, da hamayya ka iya faruwa a lokaci daya.

Mr. Rouhani ya rubuta wannan sharhi ne kwanaki kadan kafin yayi ziyarar shi ta farko a matsayin shugaba a idanun duniya, inda zai hallarci babban zauren shawarwari na MDD a birnin New York.
XS
SM
MD
LG